Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile
Legit.ng Hausa

@legitnghausa

Legit.ng (tsohuwar NAIJ.com) - Sahihiya kuma amintacciyar jaridar da ke kan gaba wajen kawo maku labaran siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi da sauransu.

ID: 796789951522373632

linkhttps://hausa.legit.ng/ calendar_today10-11-2016 19:01:42

103,103K Tweet

277,277K Followers

243 Following

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

"Sai Tinubu": Sarkin Daura ya nuna goyon bayansa ga mai girma Bola Ahmed Tinubu. Alhaji Umar Farouk Umar ya nuna cewa a 2027 suna goyon bayan shugaban ƙasa. hausa.legit.ng/news/1665154-s…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

'Ba gaskiya ba ne' Salihu Tanko Yakasai ya ƙaryata labaran da ake yaɗawa kan Abdullahi Umar Ganduje. Hakan ya biyo bayan ƴada cewa an kwantar da shi a asibitin London saboda tsananin rashin lafiya. hausa.legit.ng/news/1665201-b…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

An cafke Okpara Paul Chigozie, rikakken mai safarar kwayoyi a Najeriya. Okpara, mai shekaru 60, ya shafe shekaru 6 yana boyewa hukuma, sai yanzu dubunsa ta cika. An samu kilo 9.4 na hodar iblis da kilo 2.2 na methamphetamine a gida da motar dillalin. legit.ng/1665200-dubu-t…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

"Ya taka rawar gani" Fasto Tunde Bakare ya bayyana yadda Awujale na Ijebu, Oba Sikiru Adetona, ya assasa kafa APC. Ya nuna cewa da ba don ya yi hakan ba, da APC ba ta samu ba. hausa.legit.ng/news/1665252-a…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

An samu hargitsi a Abuja. Ƴan sanda sun buɗe wuta kan masu zanga-zanga. An raunata wasu daga cikinsu bayan sun fito adawa da rushe gidajensu. hausa.legit.ng/news/1665310-y…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

"Ba za mu manta ba" Sarkin Daura ya nuna goyon bayansa ga tazarcen mai girma Bola Tinubu. Alhaji Umar Farouq Umar ya bayyana cewa shugaban ƙasan ya karrama Muhammadu Buhari. hausa.legit.ng/news/1665399-s…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

'Yan sanda sun gudanar a gagarumin samame a sassan jihar Adamawa. Jami'an sun kama 'yan fashi, masu garkuwa da mutane, fyade, safarar yara da sauransu. Bayan cafke masu aikata laifuffuka 567, 'yan sanda sun ceto yara 13 da aka yi safararsu. legit.ng/1665483-yan-sa…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

"An keta doka" Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta taso Godswill Akpabio a gaba. Ta yi kalamai masu kaushi a kansa bayan an han ta shiga majalisar dattawa. hausa.legit.ng/news/1665486-s…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

Sanata Natasha Akpoti ta yi raddi kan hana ta shiga majalisa. Ta zargi Godswill Akpabio da take doka. Hakan na zuwa ne bayan yunƙurinta na komawa bakin aiki ya gamu da cikas. hausa.legit.ng/news/1665495-s…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

Saboda girmamawa" Majalisar dattawa za ta karrama Muhammadu Buhari. Za ta yi zama na musamman don karrama shugaban ƙasan. hausa.legit.ng/news/1665538-b…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

Ƴan ta'addan Boko Haram sun yi ta'asa a Borno. Miyagun sun yi awon gaba da jami'in gwamnati. Ana zargin an shirya masa wata ƙullalliya ne. hausa.legit.ng/news/1665590-y…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

"Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba" Shugaba Bola Tinubu ya ba da tabbaci kan matsalar rashin tsaro. Ya nuna cewa ganin bayan ƴan ta'adda na daga cikin abubuwan da ya tasa a gaba. hausa.legit.ng/news/1665600-a…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

Ƴan bindiga sun kai hari a Zamfara. An hallaka manoman da ke bakin aiki a gonakinsu. Miyagun sun kuma yi awon gaba da dabbobi. hausa.legit.ng/news/1665640-y…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

Gwamnan Enugu ya yi garambawul a majalisar zartarwarsa. A ranar Laraba, Gwamna Peter Mbah ya rantsar da sababbin kwamishinoni 6. Ya kuma sauya wa wasu kwamishinoni ma'aikatu yayin da ya yi masu gargadi. legit.ng/1665740-garamb…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

Daga 2013 zuwa 2025, jam'iyyar APC ta samu shugabanni 9. John Oyegun ne mafi dade kan shugabancin APC, kuma shi ya jagoranci nasarar jam'iyyar a 2015. A wannan rahoto, mun jero shugabannin APC tun daga Bisi Akande zuwa Nentawe Yilwatda da tasirinsu. legit.ng/1665909-yilwat…

Za a sha ruwan sama a wasu sassan jihohin Najeriya a yau Juma'a. NiMet ta ce wasu yankunan za su samu yayyafi ne kawai, yayin da rana za ta take a wasu. Jihohin da ruwan zai iya yin karfi tare da guguwa sun hada da Taraba, Bauchi, Yobe da Sokoto. legit.ng/1666017-yayyaf…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

“Allah ya gafarta masa, ya jikansa, ya kara masa rahama." Ciyaman din Gusau ya sanar da lokacin jana'izar marigayi Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello. Za a sallaci gawar Alhaji Ibrahim ne bayan sallar Juma'a a nan babban masallacin fadar Gusau. legit.ng/1666029-an-san…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

Ƴan sanda sun shiga tsakani a Bauchi. Wannan ya biyo bayan kona coci da yunkurin bankawa caji ofis wuta. Lamarin ya faru bayan wata Esther Gambo ta kashe yara 2 'yan shekara 7. hausa.legit.ng/news/1665986-y…

Legit.ng Hausa (@legitnghausa) 's Twitter Profile Photo

'Ba da yawunmu ba' Jam'iyyar SDP ta fitar da matsaya kan Nasir El-Rufai. SDP ta gargaɗi ƴan Najeriya ka da su amince da shi game da jam'iyyar. hausa.legit.ng/siyasa/1666075…