Sir_nagaree (@sirnagaree) 's Twitter Profile
Sir_nagaree

@sirnagaree

Your Number one phone plug
Beirut road Rabi'atu Plaza shop number 32
Kano N0: 08027308852

ID: 1535616806404096001

calendar_today11-06-2022 13:36:04

13,13K Tweet

4,4K Takipçi

1,1K Takip Edilen

Sir_nagaree (@sirnagaree) 's Twitter Profile Photo

Mutum shi yake ɗaga kansa ko ya wulaƙanta kansa. Ya ƙawata kansa da kyawawan ayyukansa, ko ya bata kansa da munanan halayen sa.

Sir_nagaree (@sirnagaree) 's Twitter Profile Photo

Wanda yake jin tsoron Allah, zai ji tausayin mutane, Kada ka raina kowa, domin Allah na iya ɗaukaka wanda ka raina sama da kai.

Sir_nagaree (@sirnagaree) 's Twitter Profile Photo

Arzuƙin Allah baya ƙarewa, yana ba kowa gwargwadon yadda yaga dama, Allah baya rasawa, kuma baya ƙyashi, duk lokacin da yaso sai ya azurta bawa.

Sir_nagaree (@sirnagaree) 's Twitter Profile Photo

Abin da ka aikata yau shine zai yi magana a madadinka gobe, ƙimarka ba ta cikin abin da ka mallaka, tana cikin abin da ka bari na alheri.

Sir_nagaree (@sirnagaree) 's Twitter Profile Photo

Wanda Allah Ya so, ba sai ya nemi suna a duniya ba, Allah zai fito da sunansa, wanda Allah Ya ƙi, ba zai sami kwanciyar hankali a zuciyar sa ba, koda ya mallaki duniya gaba ɗaya.

Sir_nagaree (@sirnagaree) 's Twitter Profile Photo

Fushi yana kawo hanzari da rashin natsuwa.A lokacin fushi, mutum na iya furta ko aikata abu da zai jawo mummunan sakamako Wani lokaci, fushi na iya tarwatsa dangantaka, kawar da abokai, ko haddasa matsala a aiki ko gida duk kuwa da cewa an shafe shekaru ana gina waɗannan abubuwan

Sir_nagaree (@sirnagaree) 's Twitter Profile Photo

Idan zuciya ta nutsu, ko ƙaramin abu na iya wadatar da ita amma idan zuciya ta rikice, ko duniya gaba ɗaya ba ta isar ta.

Sir_nagaree (@sirnagaree) 's Twitter Profile Photo

Haƙuri cikin jarabawa, godiya a cikin ni’ima, adalci a cikin Rayuwa, da tausayin na ƙasa sune ginshiƙan rayuwa mai kyau da albarka.