Ahmad Tijjani Magaji Esq (@atm4real) 's Twitter Profile
Ahmad Tijjani Magaji Esq

@atm4real

A Barrister & Solicitor of the Supreme Court Of Nigeria.

ID: 251567434

linkhttp://ATM.com calendar_today13-02-2011 11:56:43

1,1K Tweet

1,1K Takipçi

674 Takip Edilen

Ahmad Tijjani Magaji Esq (@atm4real) 's Twitter Profile Photo

Jaha irin ta Katsina da rashin tsaro ya dabaibaye, Fatara, Yunwa da rashin ingantaccen ilimi da albashin da ba zai kashe ma ma'aikata ƙishirwa ba, itace kuma ake murnar ƙarya da dariya ta yaudara anace ma Shugaban ƙasa bamu da ƙorafi🥲 Babu ranar da ba za'a kashe wani ba ko a

Ahmad Tijjani Magaji Esq (@atm4real) 's Twitter Profile Photo

Babu dalilin haɗa Shata da Rarara sai ga ƴan zamani da sarewa ke burgewa! Hikima ce mai zurfi a waƙoƙin zube dake bayanin al'adu na gaske, jarunta da zurfin tunani saɓanin rubutattun waƙoƙin zamani masu Edita da Manaja 😊 Ɗan Baiwa dame hikimar tsara zance a rubuce!

Ahmad Tijjani Magaji Esq (@atm4real) 's Twitter Profile Photo

Matsalar shaye shaye da sara suka cikin Matasa a yau akwai tashin hankali! Dole al'umma tayi da gaske a lokacin da ƴan ta'adda suke ƙara kusanto cikin gari bayan mamaye ƙauyuka da hanyoyi. Mudaina mafarkin gwamnati zatayi mana!

Ahmad Tijjani Magaji Esq (@atm4real) 's Twitter Profile Photo

We are often quick to speak and highlight our problems, but we lack the commitment and dedication needed to find lasting solutions. Unless we change this attitude and take responsibility, we will remain trapped in a cycle of challenges with no clear way out.

Ahmad Tijjani Magaji Esq (@atm4real) 's Twitter Profile Photo

Karmu manta da yima Sayyiduna RasululLahi SallalLahu Alaihi Wa Alihi Wasallam Salati acikin wannan dare mai albarka na Juma'a da yawan ambaton Allah a yinin Eid! Barkanmu da Shan ruwa!

Ahmad Tijjani Magaji Esq (@atm4real) 's Twitter Profile Photo

Babu wani alkhairi sama da haɗuwar kan al'ummar Sayyiduna RasululLahi SallalLahu Alaihi Wa Alihi Wasallam kuma zamu ci gaba da kira matuƙar muna numfashi! Yardar Allah ce muke nema ba ta kowa ba; Shiyasa bamu tsoron zargin mai zargi ko hassadar mai hassada!

Babu wani alkhairi sama da haɗuwar kan al'ummar Sayyiduna RasululLahi SallalLahu Alaihi Wa Alihi Wasallam kuma zamu ci gaba da kira matuƙar muna numfashi!

Yardar Allah ce muke nema ba ta kowa ba; Shiyasa bamu tsoron zargin mai zargi ko hassadar mai hassada!
Ahmad Tijjani Magaji Esq (@atm4real) 's Twitter Profile Photo

A wani bincike na Shekarar 2025 ya nuna adadin Musulmai a duniya yakai ƙiyasin 2.5 Billions wanda za'a iya cewa kaso 25 cikin 100 na Mutanen duniya. Idan ka ce masu bin aƙidarkane kaɗai musulmai, ku nawa ne a cikin musulmin Duniya?

Ahmad Tijjani Magaji Esq (@atm4real) 's Twitter Profile Photo

"Don mutum bai KULA ka ba lokacin wadatarsa ba, idan YAZO maka lokacin ƙuncinsa, kada ka kore shi. Maimakon haka ka godewa Allah da ya sanya wajen ka aka zo, ba kai kaje ba." - Prof. Ibrahim Maqari