Dr Jameel Muhammad Sadis(@DrJameelMSadis) 's Twitter Profileg
Dr Jameel Muhammad Sadis

@DrJameelMSadis

PhD Quranic Sci @iu_Madinah|
PGD Int. Buss. Studies @SOAS, London|
MSc Islamic Fin. & Mgt Durham/
DD Financial operations @AUNigeria|

كن جميلا ترى الوجود جميلا

ID:1493949989038473219

calendar_today16-02-2022 14:06:57

106 Tweets

19,7K Followers

10 Following

Dr Jameel Muhammad Sadis(@DrJameelMSadis) 's Twitter Profile Photo

DAGA TASKAR ALQUR'ANI...!!!

Gwargwadon yadda zuciyarka ta san Allah gwargwadon qarfin imaninka. Qarfin imaninka kuwa shi ke baka kyakkyawan dogaro ga Allah cikin dukkan lamuranka.

(قُلْ هُوَ ٱلرَّحْمَٰنُ ءَامَنَّا بِهِۦ وَعَلَيْهِ تَوَكَّلْنَا)

Jameel M. Sadis

account_circle
Dr Jameel Muhammad Sadis(@DrJameelMSadis) 's Twitter Profile Photo

Allah ya shiga cikin lamuranka Daddy Waziri Atiku Abubakar, yasa ka zama sanadiyyar alheri ga al'ummah. Allah ya fuskantar da zuciyarka zuwa abin da yake so kuma ya yarda dashi. Ameen.

Allah ya shiga cikin lamuranka Daddy Waziri @atiku, yasa ka zama sanadiyyar alheri ga al'ummah. Allah ya fuskantar da zuciyarka zuwa abin da yake so kuma ya yarda dashi. Ameen.
account_circle
Dr Jameel Muhammad Sadis(@DrJameelMSadis) 's Twitter Profile Photo

A cikin karanta ALQUR'ANI da sauraronsa akwai wata rayuwa ta musamman. Yi qoqari ka shiga wannan rayuwar; domin rasa ta mutuwa ce a rayuwa.

Jameel Muhammad Sadis

account_circle
Dr Jameel Muhammad Sadis(@DrJameelMSadis) 's Twitter Profile Photo

Idan ka tuno da ni'imomin da Allah ya kewaye rayuwarka dasu; sai kawai kaji kana jin kunyar saba ma Allah. Wannan wani lungu ne mai zurfi a cikin alaqar zuciya da mahaliccinta.

Jameel Muhammad Sadis.

account_circle
Dr Jameel Muhammad Sadis(@DrJameelMSadis) 's Twitter Profile Photo

Da yawa daga cikin ni'imomin qarshen zamani suna zuwa ne tare da sauqaqe hanyoyin sabon Allah. Bayin Allah na qwarai kullun qoqarinsu shi ne yin amfani da ni'imomin wajen neman yardar Allah.

Jameel

account_circle
Dr Jameel Muhammad Sadis(@DrJameelMSadis) 's Twitter Profile Photo

RA'AYI RIGA:

Kamar yadda ba kowa ce riga ce za ta yi daidai da kai ba; haka abun yake a rayuwa, ba duk ra'ayin mai sanya rigar ne zai yi daidai da kai ba. Yi qoqari ka fahimci abun da yake maslaha a rayuwarka.

Jameel Muhammad Sadis

account_circle
Dr Jameel Muhammad Sadis(@DrJameelMSadis) 's Twitter Profile Photo

Daga cikin hanyoyi masu sauqi wajen gane lafiyar zuciya da tsarkinta; tambayar zuciyar abun da take ji idan taga wani yana ci gaba a rayuwa ko yana samun alheri. Da kuma yadda take ji idan wani ya shiga damuwa.

Allahumma salli wa sallim ala nabiyyina Muhammad.

Jameel M. Sadis

account_circle