TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profileg
TRT Afrika Hausa

@trtafrikaHA

Afirka tsantsarta

ID:1560178770832678912

linkhttps://www.trtafrika.com/ha calendar_today18-08-2022 08:16:48

5,5K Tweets

41,7K Followers

24 Following

TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Yaƙi na tsawon shekara guda ya kekketa Sudan, tun bayan da tsamin dangantaka tsakanin rundunar sojin ƙasar da rundunar ɗaukin gaggawa ta ƙasar RSF, ta haifar da ɓarkewar arangama a titunan birnin Khartoum a tsakiyar watan Afrilun 2023.

buff.ly/49BW0g6

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

An soka wa wani bishop tare da wasu mutanen uku wuƙa a lokacin da yake huduba a Cocin Christ the Good Shepherd a Sydney.
‘Yan sanda sun ce an kama wani mutum, sannan raunin da Bishop Emmanuel ya ji ba mai hadari ba ne.

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Batun Cyprus da safarar teku cikin aminci a Bahrul Aswad na daga cikin batutuwan da aka tattauna, a cewar majiyar.

buff.ly/3VX3Jly

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a tattaunawarsa ta waya da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani:
- Musulmai na buƙatar ƙara ƙoƙari wajen haɗin kansu don dakatar da hare-haren cin zali na Isra'ila
- Yin aiki da hankali yana da muhimmanci don hana yaɗuwar tashin…

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a tattaunawarsa ta waya da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani: - Musulmai na buƙatar ƙara ƙoƙari wajen haɗin kansu don dakatar da hare-haren cin zali na Isra'ila - Yin aiki da hankali yana da muhimmanci don hana yaɗuwar tashin…
account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Harin ramuwar gayya da Iran ta kai wa Isra’ila a ranar Asabar ɗin da ta gabata ya dugunzuma duniya inda wasu ke fargaba game da yiwuwar ɓarkewar sabon yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya da ma tsoron ɓarkewar Yaƙin Duniya na Uku
Ga Shamsiyya Hamza Ibrahim da sharhi kan batun.

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Shugaban Chadi na riko Mahmet Deby ya ce ya cika alkawuran da ya yi wa kasar. Ya bayyana haka ne a lokacin da ya kaddamar da yakin neman zaben kasa da za a yi a watan gobe. Ya hau mulki ne a 2021 bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Deby wanda ya shafe shekara 30 yana mulki.

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

An samu rabuwar kawuna tsakanin mambobin majalisar ministocin Isra'ila kan ma'auni da kuma lokacin da ya kamata a kai wa Iran hari.

buff.ly/3JhLPCD

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Mutanen sun mutu ne a hanyarsu ta komawa Gombe daga Azare inda suka je kai kayan aure a ranar Lahadi
Gwamnan jihar Gombe Alhaji Inuwa Yahaya da Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar na cikin waɗanda suka halarci jana’izar da aka yi a birnin Gombe a yau Litinin

Mutanen sun mutu ne a hanyarsu ta komawa Gombe daga Azare inda suka je kai kayan aure a ranar Lahadi Gwamnan jihar Gombe Alhaji Inuwa Yahaya da Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar na cikin waɗanda suka halarci jana’izar da aka yi a birnin Gombe a yau Litinin
account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Sakataren Majalisar DInkin Duniya Antonio Guterres ya nemi kasashen Iran da Isra’ila da su kai zuciya nesa kuma su girmama dokokin kasa da kasa.

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

A yayin da aka cika shakara 10 da sace ƴan matan makarantar Chibok 276 a jihar Borno da ke Nijeriya, iyayen sauran matan da har yanzu ba a gan su ba sun bayyana halin ƙuncin da suke ciki tare da jaddada kiransu ga gwamnatin ƙasar ta kuɓutar da ‘ya’yansu.
👇trtafrika.com/ha/africa/shek…

A yayin da aka cika shakara 10 da sace ƴan matan makarantar Chibok 276 a jihar Borno da ke Nijeriya, iyayen sauran matan da har yanzu ba a gan su ba sun bayyana halin ƙuncin da suke ciki tare da jaddada kiransu ga gwamnatin ƙasar ta kuɓutar da ‘ya’yansu. 👇trtafrika.com/ha/africa/shek…
account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Dakarun Isra'ila sun yi luguden wuta a kan wasu Falasɗinawan Gaza a yayin da suke yunƙurin komawa gidajensu da ke arewacin yankin. Harin ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum biyar, ciki har da mata da ƙananan yara, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa Anadolu Agency.

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

'Yankin Gabas ta Tsakiya yana cikin yiwuwar faɗawa cikin bala'i,' kamar yadda Antonio Guterres ya shaida wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya. buff.ly/3vUfVc9

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Jakai suna cikin dabbobi da Hausawa suka daɗe suna amfani da su wurin sufuri. Sai dai yanzu tsadar da suka yi ta jefa fargabar a zukatan masu sayar da su da ma masu amfani da su, kamar yadda suka yi wa TRT Afrika Hausa bayani a kasuwar Ma'Adua ta jihar Katsina a Nijeriya

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Daraktan hukumar leƙen asirin Amurka, CIA, William Burns ya tuntuɓi takwaransa na Turkiyya Ibrahim Kalin lokacin bukukuwan ƙaramar Sallah inda ya roƙe shi ya taimaka wajen yin sulhu game da rikicin Gabas ta Tsakiya. buff.ly/3Q35l9s

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Wannan sakamakon ya hana Liverpool mai maki 71 hayewa teburin gasar Firimiya inda take ta uku a bayan Manchester City wadda take da maki 73 da kuma Asernal mai maki 71. buff.ly/4aB9utG

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Na'urorin Isra'ila da ke kakkaɓo makamai sun tare jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da Iran ta harba, kamar yadda wannan bidiyo da aka naɗa a birnin Ramallah da ke Yammacin Birnin Ƙudus da aka mamaye, ya nuna.

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Ƴan ƙasar Sudan kimanin miliyan ɗaya ne suka tsallaka zuwa Chadi tun da aka soma yaƙi tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai ɗaukin gaggawa na Rapid Support Forces a watan Afrilun 2023. buff.ly/4aT16p1

account_circle
TRT Afrika Hausa(@trtafrikaHA) 's Twitter Profile Photo

Da alama makaman da Iran ta harba sun sauka a filin jirgin saman Ramon da ke yankin Negev, a yayin da ta ƙaddamar da hare-hare na jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami fiye da 200 a Isra'ila ranar Asabar da tsakar dare.

account_circle